Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya za ta baiwa masu karamin karfi gidaje

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya za ta baiwa masu karamin karfi gidaje

- Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu, ta ce kwanan nan za ta kaddamar da gidaje mai sassa 48 a karkashin shirin gidaje mai suna ‘Rent-to-Own project’

- An tattaro cewa masu karamin karfi ne za su amfana daga wannan shiri

- Mukaddashin manajan daraktan na ma’aikatar gidaje ta tarayya, Umar Gonto, ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin Shugabar SERVICOM, Nnenna Akajemeji

Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu, ta ce kwanan nan za ta kaddamar da gidaje mai sassa 48 a karkashin shirin gidaje mai suna ‘Rent-to-Own project’ ga masu karamin karfi a fadin yankunan kasar guda shida.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mukaddashin manajan daraktan na ma’aikatar gidaje ta tarayya, Umar Gonto, ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin Shugabar SERVICOM, Nnenna Akajemeji.

Gonto ya kuma bayyana cewa yan Najeriya musamman masu karamin karfi, za su ci moriyar shirin sosai.

Yayinda ta ke bayanin dalilin ziyararta, shugabar SERVICOM ta bayyana cewa ta so ne ta jadadda yara da dokokin ofishin sakataren gwamnatin tarayya wanda ya bayyan cewa dole dukkanin jagorori da sassa na hukumar su yi aiki a karkashin shugabanni da manajan daraktansu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Za a yi rikici idan arewa ta kafe a kan sake yin takarar shugaban kasa - Dattijan kudu

Ta kara da cewa biyo bayan umurnin, hakan zai kawo karshen kalubalen da ake fuskanta wajen samun ganin manyan shugabanni sannan kuma cewa hakan zai sa sassan su yi aiki yadda ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel