Kwace kujerar Gwamnan Imo: Masoya Ihedioha sun gudanar da zanga mai sosa zuciya, sun zargi Tanko da kisan Dimokradiyya
Masoya da masu goyon bayan tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, da kotu ta kwace kujerarsa, sun mamaye titunan Owerri, babban birnin jiha, domin nuna adawarsu a kan hukuncin da kotun koli ta zartar a makon jiya.
Masu zangar, maza mata, matasa da dattijai, sun bukaci kotun koli ta warware hukuncin data yanke tare da neman a mayar wa da Ihedioha kujerarsa ta gwamna domin shine zabinsu.
A ranar Talata ne kotun koli ta zartar da hukuncin karbe kujarar Ihedioha tare da bawa hukumar zabe ta kasa (INEC) umarnin mika shahadar samun nasarar lashen zabeb kujerar gwamna ga dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma.
Sanata Uzodinma, dan takarar jam'iyyar APC, shine ya zo na hudu a zaben kujerar gwamnan jihar Imo da aka yi a shekarar 2019, kamar yadda INEC ta sanar.
DUBA WANNAN: Kano: Mahaifin Sulaiman ya gindaya wa Ba Amurkiyar data zo auren dansa sharudda guda 4
Masu zanga -zangar na dauke da manyan takardu da rubutattun sakonni daban - daban dake nuna adawarsu da rashin jin dadinsu a kan hukuncin da kotun koli ta zartar a kan Ihedioha.
Wasu daga cikin irin sakonnin da masu zangar - zangar ke dauke dasu sun bayyana cewa, "a dawo ma da shi," "shine zabinmu", "Tanko ya kashe dimokradiyya", da sauransu.
Yawancin masu zangar - zangar na sanye da bakaken kaya, wata alama dake nuna suna cikin bakin ciki. Duba hotuna a kasa:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng