Dattawan Bauchi sun roki jama’a da su amince da hukuncin kotun koli ba tare da rigima ba

Dattawan Bauchi sun roki jama’a da su amince da hukuncin kotun koli ba tare da rigima ba

- Kungiyar dattawa don zaman lafiya da shugabanci nagari a jihar Bauchi, sun roki al’umman jihar da su yarda da duk yadda hukuncin kotun koli zai kaya

- Sarkin Arewan Bauchi, Alhaji Hassan Sherif, ya ce rokon ya zama dole duba ga halin fargaba da ake ciki a jihar yayinda kotun ke shirin zartar da hukunci

- Haka kuma wata kungiyar matasa ta yi kira ga yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji tunzura lamarin gabannin hukuncin kotun koli

Gamayyar kungiyar dattawa don zaman lafiya da shugabanci nagari a jihar Bauchi, sun roki al’umman jihar da su yarda da duk yadda sakamakon hukuncin kotun koli zai kaya a kan zaben gwamna wanda aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Wani jawabi dauke da sa hannin Sarkin Arewan Bauchi, Alhaji Hassan Sherif, da wasu 20 a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu, ya ce rokon ya zama dole duba ga halin fargaba da ake ciki a jihar yayinda kotun ke shirin zartar da hukunci.

Ya bayyana cewa an san jihar da zaman lafiya da kuma hakuri kan lamarin siyasa tun a jumhuriya na biyu lokacin da wadanda suka sha kaye suka je kotu don neman mafita, cewa hukuncin kotun bai tayar da fitina ko rikici ba a jihar don haka akwai bukatar cigaba da hakan.

Hazalika, Wata kungiyar jama’a a jihar, Arewa Youth Mobilization and Mass Mobilization for Voting Wisely, ta yi kira ga yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji tunzura lamarin gabannin hukuncin kotun koli.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Sokoto: PDP da APC sun nuna karfin gwiwar samun nasara a kotun koli

Da yake jawabi ga Manama labarai a Sakatariyar NUJ a Bauchi, kakakin kungiyar Abdullahi Abdulkadir ya bukaci jami’an tsaro da su zama cikin shiri a jihar domin gudun take doka da oda bayan hukuncin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel