Ikpeazu ya maidawa Frank raddi a kan bin Tagawar Buhari zuwa Turai
Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya maidawa Timi Frank raddi mai zafi a game da sukar sa da ya yi na bin shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa wani taro a kasar Ingila.
Okezie Ikpeazu ya maida martani ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Enyinnaya Appolos, a wani dogon jawabi da ya fitar a Ranar 14 ga Junairun 2020.
Gwamnan ya ke cewa Timi Frank bai taba zama ‘Dan jam’iyyar PDP ba, sai dai kawai gantalin siyasa, tare da cewa ya na cikin wadanda su ka kai Goodluck Jonathan, su ka baro shi.
Komai da lokacin sa, amma a cewar Gwamnan, “Timi Frank, wanda ya sha kunya a matsayin Mai magana da yawun bakin APC, bai da lokacin komai sai dai neman mafakar siyasa.”
“A dalilin haka aka fatattake shi daga kujerar Kakakin APC, bayan aikinsa ya kare na kawowa tazarcen Goodluck Jonathan da gwamnatin PDP da kafa gwamnatin APC ta Buhari.”
KU KARANTA: Gwamnonin PDP su na yi wa Jam'iyya zagon-kasa - Frank
“Abin da ya faru shi ne an yi amfani da shi, an jefar da shi. Frank saniyar ware ne a PDP a lokacin zaben 2019, domin babu abin da ya sa gaba sai abin da zai samu a wajen Atiku.”
Appolos ya ce irinsu gwamna Ikpeazu kuwa su ne su ka dage wajen ganin PDP ta kai ga nasara har PDP ta zarce a Abia. Appolos ya kuma yi wa Frank gorin yi wa APC aiki a 2015.
Mista Appolos ya kare tafiyar da aka yi da gwamnan, inda ya ce tun kafin hukuncin zaluncin zaben Imo, aka shirya wannan tafiya zuwa taron ‘Yan kasuwan Birtaniya da Afrika a Ingila.
“Nauyin mutanen Abia ne ya rataya a kan shi kafin komai.” Sannan Hadimin ya nuna cewa ba dadin jirgi ta sa gwamnan ya bi Tawagar Buhari ba, sai dai habaka kasuwancin jihar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng