Yakubu Gowon ya na maraba da shugabancin Ibo idan zai kawo zaman lafiya
Yunkurin mutanen kasar Kudu maso Gabashin Najeriya na fito da shugaban kasa ya gamu da hobbasa daga wajen wani tsohon shugaban kasa.
Janar Yakubu Gowon ya nuna cewa ya na goyon bayan mutanen Ibo su tsaida wanda zai zama shugaban kasa a Najeriya a zabe na gaba da za ayi.
A daidai lokacin da aka fara huro wuta game da 2023, Yakubu Gowon ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da gidan rediyon BBC Hausa.
Janar Gowon ya ke cewa samun shugaban kasa daga Kabilar Ibo, lamari ne da za ayi lale da shi, tare da cewa saken da aka yi ne ya hana Ibo mulki.
KU KARANTA: Ubah: Zan yi nasara a kotun daukaka kara inji Sanatan Anambra

Asali: Depositphotos
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa da ace an cigaba da tsarin kama-kama da aka fara a PDP, da kawo yanzu Ibo sun samu damar rike Najeriya.
“Idan har hakan zai kawo zaman lafiya, to sai ayi; Idan har jama’a su na so.” Dattijon kasar ya shaidawa gidan rediyon wannan a wata hira.
Jam’iyyar PDP ta saki layin da ta kama na kama-kama a lokacin da Goodluck Jonathan ya dare a kan mulki bayan rasuwar Ummaru ‘Yaradua.
Kwanan nan ne wani Dattijon kasar, Tanko Yakasai, ya fito ya na cewa idan aka marawa Inyamurai baya, za su iya fito da shugaban kasa a 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng