Buhari ya saka baki a kan hukuncin kisa da Saudiyya ta zartar a kan Malamin Islama dan Najeriya

Buhari ya saka baki a kan hukuncin kisa da Saudiyya ta zartar a kan Malamin Islama dan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari'a, Abubakar Malami da ya duba matsalar Ibrahim Ibrahim, malamin Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a kasar Saudi Arabia.

Buhari ya bada wannan umarnin ne bayan da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya rokesa a kan ya duba lamarin malamin addinin dan asalin jihar Zamfara.

Kamar yadda takardar da Zailani Bappa, mataimaki na musamman ga Matawalle ya bayyana, an saka Ibrahim cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a kan laifin safarar miyagun kwayoyi.

"A jiya ne Gwamna Matawalle ya hadu da Shugaba Muhammadu Buhari a kan hukuncin da aka yi wa Ibrahim a makon da ya gabata, a kan safarar miyagun kwayoyi," cewar takardar.

"An yankewa Ibrahim hukuncin kisa a gaban kotun da ke Saudi Arabia saboda rashin lauya. Kotu biyu a Jedda suka wankesa saboda rashin shaida daga masu gurfanarwa.

"Amma kuma sai masu gurfanarwar suka daukaka kara a Makkah inda ake bukatar ganin lauyansa ko a yanke mishi hukuncin kisa.

DUBA WANNAN: Basirar 'yan Najeriya: Matashi ya kirkiri injin bayar da wutar lantarki mai amfani da ruwa, ba fetur ba

"A halin yanzu, shugaban kasa Muhammad Buhari ya umarci ministan shari'a, Abubakar Malami da ya yi abin da ya dace don tseratar da ran Ibrahim Ibrahim." in ji takardar.

A watan Afirilu na 2019 ne hukumomi suka saki Zainab Aliyu, daliba a jami'ar Bayero dake Kano bayan gwamnatin Najeriya ta sa baki.

An kama Aliyu ne tare da garkameta saboda safarar miyagun kwayoyi amma gwamnatin kasar Saudi Arabia ta yi bincike kuma ta sake ta bayan ta gano bata da laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel