Tsautsayi ba a sa maka rana: Zakara ya kashe wani mutumi

Tsautsayi ba a sa maka rana: Zakara ya kashe wani mutumi

- Saripalli Venkateswara mai shekaru 55 ya hadu da ajalinshi ne sakamakon fadan kaji wanda aka yi a bikin Makar Sankranti a kasar Indiya

- Ya rike kazar ne daure da wuka kafin ya sake ta ta fara fada da 'yar uwarta, amma sai tayi kokarin kwace kanta lamarin da ya jawo wukar ta soke shi a ciki

- Tuni kotun kolin kasar Indiya ta haramta wannan lamarin don ya saba jawo raunika ga jama'a a yayin bikin Makar Sankranti

Wani mutum mai shekaru 55 ya rasa ran shi bayan da wata kaza daure da wuka mai kaifi ta soke shi a ciki yayin fada a wata liyafar dare a Indiya.

Anyi fadan ne a kauyen Pragadavaram dake Yammacin Godavari a jihar Andhra Pradesh duk da kuwa kotun kolin kasar ta haramta hakan.

Mashiryan liyafar sun daura wuka mai kaifi ne a kafar kazar, inji 'yan sanda.

Wanda abun ya ritsa dashi na rike da dabbar ne a hannun shi, yana jiran ya saketa fili don fada. Amma sai kazar tayi kokarin guduwa amma sai wukar ta soki cikin shi wanda hakan yayi ajalin shi.

KU KARANTA: Trump ya dauko hayar manyan lauyoyi da za su hana a tsige shi

Jaridun yankin sun bayyana sunan mamacin da Saripali Venkateswara Rao mai shekaru 55. Mutuwar shi kuwa ta zo ne bayan kotun kolin kasar Indiya ta haramta fadan kaji kuma ta bayyana shi a zaluntar dabbobi wanda karantsaye ne ga dokokin hakkokinsu na 1960.

Kafin a haramta hakan, mutane 10 sun raunata a kauyen Kavvagunta dake Yammacin Godavari yayin da mutane masu yawa suka raunata a kauyen Chintam Palli sakamakon fadan kaji.

A Indiya, fadan kaji na daga cikin murnar bikin Makar Sankranti, biki ne da ake sadaukar dashi ga ubangiji Surya na ma'abota addinin Hindu. Anyi bikin Makar Sankranti a wannan shekarar ne a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel