Na aureshi a lokacin yana makaho, amma yanzu da ya fara gani yace zai sake ni saboda ni mummuna ce

Na aureshi a lokacin yana makaho, amma yanzu da ya fara gani yace zai sake ni saboda ni mummuna ce

- Wata mata mai shekaru 36 ta shiga kunci da kunar rai saboda ita mummuna ce

- Stella ta auri mijinta ne lokacin yana makaho kuma tana matukar kaunar shi amma yana warkewa yace bai san wannan ba

- A cewar shi, so makaho ne kuma wannan makantar ce tasa ya auri mummunar mace, don haka yana bukatar saki

Wata mata ta shiga kunci da kunar rai saboda ita mummuna ce. Kamar yadda tace, ta auri mijinta ne a lokacin yana makaho amma yanzu da ya samu waraka daga makanta, sai ya bukaci saki. Ga labarin dalla-dalla.

"Sunana Cynthia kuma ina da shekaru 36. Na auri mijina ne ba don kudi ba sai saboda soyayya. Duk da kuwa iyayenshi ne suka rokeni na aure shi, amma ina son shi.

"Na aureshi lokacin yana makaho kuma na dinga nema mishi magani. Bayan shekaru biyu aka yi mishi aikin ido cike da nasara. Da kudina wanda na aro daga kamfani aka yi mishi aikin.

KU KARANTA: Amfanin kiwon mage a gida ga mutane

"Bayan mako daya sai ya samu ido amma sai ya bar gida. Naji labarin yayi sabuwar budurwa wacce ya tare wajenta. Wata rana ya shigo gida ya bayyana kalaman da suka bani mamaki."

Kamar yadda mijin yace mata "soyayya makauniya ce, wannan makantar ce tasa na auri mummunar mace. A yanzu idona biyu don haka ba zan zauna dake ba."

"Me nayi wa wannan butulun da bai san halacci ba. Gaskiya ina tunanin watsa mishi acid don in lalata halittar shi. Ina bukatar shawara." Cewar mummunar matan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel