Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa birnin London (Hotuna)

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya isa birnin London (Hotuna)

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya isa birnin London da ke Ingila domin hallarton taron zuba jari na na Afirka da Burtaniya da za a gudanar a ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

A baya, hadiman shugaban kasar ya sanar da cewa shugaban kasar zai yi wannan tafiyar tun a ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Kudin yanka: Malami ya damfari mabiyansa N4.3m

A cewar masu shirya taron, Farai ministan Burtaniya, Boris Johnson ne ake sa ran zai zama mai masaukin baki inda ake sa ran shugabanin Afirka da shugabanin kamfanoni na kasa da kasa su hallarci taron.

Tawagar Najeriya da za ta hallarci taron za ta nuna wa duniya irin sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi da hanyar kirkiran sabbin dokoki da za su inganta kasuwanci a kasar.

Wannan shine karo na farko da shugaban kasar ya fita kasar waje a 2020 kuma gwamnonin da suka yi masa rakiya sun hada da Yahaya Bello na jihar Kogi, Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sauran wadanda suka tafi tare da shugaban kasar sun hada da Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Masana'antu, kasuwanci da saka jari, Otunba Niyi Adebayo, Ministan Kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed; Mai bawa shugaban kasa shawara a fanin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (murabus) da shugaban NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a ranar Alhamis mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel