Ihedioha: PDP ta bayyana matakin da za ta dauka bayan hukuncin kotun koli a Imo

Ihedioha: PDP ta bayyana matakin da za ta dauka bayan hukuncin kotun koli a Imo

- Jam'iyyar PDP ta bayyana matakin da za ta dauka bayan hukuncin kotun koli a kan shari'ar jihar Imo

- Jam'iyyar hamayyar ta ce za ta yi zanga-zanga kan hukuncin na kotun koli da ta bawa jam'iyyar APC nasara

- PDP ta koka kan cewa an kwace nasarar ta a jihar an sace an mika wa jam'iyyar APC

Jam'iyyar People Democratic Party (PDP) ta yi kira ga 'ya'yan ta su yi zanga-zanga a kan hukuncin kotun koli na kasa a taron shugabaninta da ta kira a ranar Juma'a 17 ga watan Janairu.

Shugaban jam'iyyar, Prince Uche Secondus ne ya yi kirar inda ya ce an sace nasarar Emeka Ihedioha.

Secondus ya bayyana hukuncin da kotun ta zartar na bayyana Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar a matsayin 'barin shari'a'.

Jam'iyyar hamayyar ta bayyana fargabar cewa idan abubuwa suka cigaba da faruwa haka a Najeriya, akwai yiwuwar kasar za ta iya tarwatse wa nan ba da dadewa ba.

Ta yi nadamar cewa bayan da ta mika mulkin kasar ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a 2015, duk lamuran kasar sun tabarbare.

DUBA WANNAN: Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

Da ya ke tsokaci a kan batun, shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, Sanata Walid Jibrin ya ce: "Jam'iyyar mu ta yi mulki mai kyau daga 1999 zuwa 2015."

"A matsayinmu na masoya demokradiya na gaskiya, mun mika wa jam'iyyar da ke mulki ragamar kasar muna fatan hakan zai inganta demokradiyya amma daga bisani sun gamu da takaici."

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa jam'iyyar ta PDP ta bukaci a saki bitan shari'ar na kotun koli a kan zaben gwamnan jihar Imo na korar Emeka Ihedioha duba da cewa ba ta gamsu da hakan ba.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu a taron manema labarai da ta kira a sakteriyarta da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel