Gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Buju Bazamfare ya mika kansa a Nasarawa

Gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Buju Bazamfare ya mika kansa a Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da ke jihar, Buju Bazamfare ya mika kai kuma ya ajiye makamansa.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar godiya da ya kai wa Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu a Abuja a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya yabawa 'yan sanda a jihar, musamman kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe da tawagarsa saboda tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar, inda ya fadawa IGP din cewa ya yi ido biyu da mai garkuwa da mutanen da wasu da suka amince su ajiye makamansu.

Gwamnan ya shaidawa IGP cewa, "An fada min yayin taron cewa sun amince za su gana da kai ido da ido kuma su mika maka makamansu tare da mika kansu."

Gwamnan ya ce wannan babban nasara ce a jihar a yunkurin rage laifuka kuma ya godewa IGP kan gudunmawar da ya ke bawa jihar.

DUBA WANNAN: Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

A bangarensa, IGP Adamu, ya bayyana a wurin taron tsaro na Arewa maso tsakiya da za a gudanar a Lafia a ranar 22 ga watan Janairu inda masu ruwa da tsaki za su hadu da suka hada da masu sarautun gargajiya, 'yan banga, shugabanin siyasa da sauran hukumomin tsaro don tattaunawa kan matsalolin tsaro da ke adabar yankin.

IGP na 'yan sandan ya ce cikin abubuwan da za a tatauna a wurin taron sun hada da batun 'yan sandan unguwanni da ake sa ran aiwatarwa a wannan shekarar inda ya ce tsarin ba wai na yanki bane amma na kasa baki daya.

Ya yi bayanin cewa, "Shiri ne da za a gudanar a garuruwa tare da hadin kan dukkan mutanen gari daga kauyuka zuwa mazabu da kananan hukumomi zuwa matakin jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel