Akwai yiwuwar hana Father Mbaka yin wa'azi - Babban limamin katolika

Akwai yiwuwar hana Father Mbaka yin wa'azi - Babban limamin katolika

- Babban limamin cocin Katolika da ke Legas, Adewale Martins, ya ce akwai yiwuwar hana Rev Father Ejike Mbaka na cocin Adoration Ministry yin wa'azi

- Martins ya ce hakan za ta kasance ne idan har Mbaka ya ci gaba da irin salon yadda yake gudanar da wa'azinsa da ya kauce wa tanade-tanaden akidar katolika

- Hakkan martani ne ga hasashen da Mbaka ya yi na cewa Sanata Hope Uzodinma zai zama gwamnan jihar Imo

Rahotanni sun kawo cewa akwai yiwuwar hana Rev Father Ejike Mbaka na cocin Adoration Ministry yin wa'azi, idan har ya ci gaba da irin salon yadda yake gudanar da wa'azinsa da ya kauce wa tanade-tanaden akidar katolika.

Babban limamin cocin Katolika da ke Legas, Adewale Martins ne ya bayyana haka a hira da sashin BBC.

Martins wanda fafaroma ya nada a matsayin babban limamin cocin ta katolika a shekarar 2012, ya bayyana cewa dole ne Father Mbaka ya daina 'wuce gona da iri'.

babban faston na martani ne kan hasashen da Mbaka ya yi na cewa Sanata Hope Uzodinma zai zama gwamnan jihar Imo wanda kuma hakan ce ta kasance, bayan kotun koli ta kwace kujerar shugabancin jihar daga hannun Emeka Ihedioha sannan ta mika masa.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Sule ya yi magana kan Amotekun, ya ce tuni suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a Nasarawa

A ranar jajiberin sabuwar shekara ne dai Mbaka ya yi hasashen cewa Hope Uzodinma zai zama gwamnan jihar Imo a shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng