Gwamna Sule ya yi magana kan Amotekun, ya ce tuni suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a Nasarawa

Gwamna Sule ya yi magana kan Amotekun, ya ce tuni suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a Nasarawa

- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya jadadda cewa kungiyoyin tsaro na sa kai sun fi inganci

- Gwamna Sule ya ce su sun jima da suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a jihar Nasarawa

- Martaninsa na zuwa ne bayan gwamnonin yankin kudancin kasar sun kafa yan sandan tsaro na yankin jihohin yarbawa wacce aka fi sani da Amotekun

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa su sun jima da suka fara aiki da kungiyoyin tsaro na sa-kai a jihar.

A cewar Sule, babu wani yanki da ke fadin jihar da basu irin wannan kungiyoyi na ‘yan banga domin samar da cikakken tsaro a jihar.

Har ila yau gwamnan ya bayyana cewa lallai jihar za ta karfafa wa irin wadannan kungiyoyi karfi domin su rika samar da tsaro mai inganci a fadin jihar, inda ya ce hakan zai taimaka wa jami’an tsaron jihar wajen aikin kakkabe miyagu masu laifi a fadin jihar.

Martanin gwamnan na Nasarawa na zuwa ne bayan gwamnonin yankin kudancin kasar sun kafa yan sandan tsaro na yankin jihohin yarbawa wacce aka fi sani da Amotekun.

Sai dai jim kadan bayan haka, ministan shari’a Abubakar Malami ya gargadi gwamnonin da su dakatar da wannan shiri na su inda ya ce hakan ya saba wa dokar kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe hakimi wani kauyen Niger, sun sace mutum 17

Wasu daga cikin gwamnonin sun fito karara inda suka bayyana cewa sun yi daidai kan abin da suka yi na kafa rundunar tsaro domin yankin yarbawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng