Gwamnati ta rabawa Matasa da Marasa karfi Biliyan 55.3 a cikin shekaru 6

Gwamnati ta rabawa Matasa da Marasa karfi Biliyan 55.3 a cikin shekaru 6

Gwamnatin tarayya ta raba Dala miliyan 155 ga marasa karfi da matasa a Najeriya a wani tsari da aka kafa a 2013 domun kauda talauci a fadin kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, an kashe wannan kudi ne daga lokacin da babban bankin Duniya ya fara taimakawa Najeriya wajen yakar talauci.

Babban bankin Duniya ya ware Dala miliyan 300 ga tsarin YESSO wanda aka kafa domin taimakawa marasa galihu da koyawa Matasa sana’a.

Kawo yanzu an kashe fiye da rabin wannan kudi watau Dala miliyan 155 a shekaru shida. Idan aka yi lissafi a kudin gida, an batar da Biliyan 55.3.

Mukaddashiyar shugabar wannan shiri na bankin Duniya, Hajiya Hajara Sani, ta shaida wannan ga Manema labarai a Ranar Laraba a Garin Abuja.

KU KARANTA: VAT ya tashi daga 5% bayan Buhari ya sa hannu a sabon kudiri

Hajara Sani ta ce mutane 500, 000 daga jihohi 16 na kaar nan ne su ka amfana da wannan kudi. Har yanzu kuma ana cigaba da wannan shiri a kasar.

A jawabin na ta na rabar 16 ga Watan Junairun 2020, Sani ta bayyana cewa lokacin da bankin Duniya ya warewa wannan shiri ya na nema ya karaso.

Akwai rukunan mutanen da ake biya N7500 duk wata, daga ciki har wasu da ake koyawa sana’ar hannu a karkashin hukumar nan ta NDE ta gwamnati.

Shugabar wannan shiri ta ce su na tallafawa mutanen Arewa maso Gabas da su ke zama a sansanin ‘Yan gudun hijira a sakamakon rikicin Boko Haram.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel