Hope Uzodinma: PDP ta bukaci Shugaban alkalan Najeriya, Tanko ya yi murabus
Bayan rashin gamsuwa da yadda kotun koli ta tsige Emeka Ihedioha daga matsayin gwamnan jihar Imo, jam’iyyar People Democratic Party (PDP), ta yi kira ga sake duba lamarin cikin gaggawa da kuma janye hukuncin kotun kolin.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jam’iyyar ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, a wani taron manema labarai a sakatariyarta da ke Abuja.
Legit.ng ta tattaro cewa yayinda ya ke jawabi ga manema labarai, Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, ya ce janye hukuncin zai kasance saboda adalci.
Kotun kolin a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, ta soke zaben Ihedioha a matsayin gwamnan jihar.
Kotun kolin ta kaddamar da Hope Uzodinma na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris a jihar.
Idan za a tuna Uzodinma ne ya zo na hudu a zaben yayinda Uche Nwosu na jamíyyar Action Alliance (AA) da Ifeanyi Ararume na jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) suka zo na biyu da uku.
Kwamitin mutum bakwai na kotun koli karkashin jagorancin Shugaban Alkalan Najeriya Tanko Muhammad suka yanke hukuncin na bazata a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, a Abuja.
Da ya ke bayyana matsayar kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, Secondus, ya ce bayan nazari sosai kan dukkanin lamarin dake kewaye da hukuncin kotun koli wanda ya bayyana a matsayin zubewar adalci, jam’iyyar ta yanke cewa a yanzu kotun koli karkashin Justis Tanko ta zama wacce ake juyawa.
KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamna Shettima ya nuna sha'awarsa ta son zama daga cikin masu juya kasa daga Abuja
Ya yi zargin cewa a yanzu an dabaibaye kotun kolin domin ta aiwatar da ajadar gwamnatin APC kan mutanen Najeriya.
Secondus ya kara da cewa ya zama dole Shugaban alkalan ya samarwa yan Najeriya amsoshin wasu tambayoyi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng