Tsohon gwamna Shettima ya nuna sha'awarsa ta son zama daga cikin masu juya kasa daga Abuja

Tsohon gwamna Shettima ya nuna sha'awarsa ta son zama daga cikin masu juya kasa daga Abuja

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ya ce a yanzu da yake Abuja zai so ace ya kasance daga cikin masu juya gwamnatin nan idan har ya samu damar.

An tatttaro cewa Shettima, wanda ya kasance sanata mai ci ya yi furucin ne a lokacin da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a Abuja.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa akwai masu juya kasa a kowace gwamnati, inda ya ce masu juya kasa sun kasance har a mulkin tsoffin shugabannin kasar Amurka Jimmy Carter da Barrack Obama.

“A lokacin da Jimmy Carter ya kasance shugaban kasar Amurka yana da nashi masu juya kasar. Ana kiransu da Georgia Gang. Kusan dukkanin wadanda ya ba mukami sun kasance daga Georgia,” inji shi.

“Ko lokacin da dan uwanmu, Barrack Obama ya zama Shugaban kasa, manyan nade-nade 16 a gwamnatin Obama sun kasance daga Chicago. Manyan ma’aikatansa biyu da sakatarori biyu sun kasance daga Chicago."

KU KARANTA KUMA: Fusatattu matasa sun yiwa soja mugun duka kan kashe wani mai siyar da takalma a Kaduna

Amma sanatan ya ce maimakon kiran wadannan mutanen da masu juya kasa zan so a kira su da masu karya mulki.

“Idan zan samu dama, yanzu da nake Abuja, zan so na shiga cikin masu juya kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel