Yanzu-yanzu: Bayan rasa jihar Imo, PDP zata yi ganawar gaggawa

Yanzu-yanzu: Bayan rasa jihar Imo, PDP zata yi ganawar gaggawa

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta shirya ganawar gaggawar majalisar zantarwanta a ranar Juma'a, 17 ga Junairu, 2020.

A sanarwan, sakataren jam'iyyar, Ibrahim Tsauri, ya ce za'a fara ganawar misalin karfe 10 na safe.

Yace: "An gayyatan dukkan mambobin majalisar zantarwan jam'iyyar PDP zuwa ganawar gaggawa gobe Juma'a, 17 ga Junairu, 2020."

"Za'a yi ganawar ne a Hedkwatar uwar jam'iyyar dake Wadata Plaza, Abuja misalin karfe 10."

"Muna kira ga mambobi su halarta domin za'a tattauna harkokin kasa."

Duk da cewa ba'a bayyana makasudin shirya ganawar ba, majiya daga sakatariyar PDP sun bayyanawa manema labarai cewa ganawar na da alaka da shari'ar kotun koli da ta fitittiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, a jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel