Ke duniya: Yaro mai shekaru 10 ya halaka wani dalibi a kan budurwa

Ke duniya: Yaro mai shekaru 10 ya halaka wani dalibi a kan budurwa

Yan sandan Bududa da ke yankin gabas na Uganda suna neman wani yaro mai shekaru 10 ido rufe, a kan sukar wani dalibi dan'uwansa da yayi da wuka sakamakon zarginsa da soyayya da budurwarsa mai shekaru 11.

Wanda ake zargin dalibi ne a makarantar firamare ta Buwali, kuma mazaunin Bunamubi Parish ne dake Bukigai., kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ya soki Sam Watsotsi mai shekaru 16 ne da wuka a kasan cibiyarsa a ranar Lahadi sakamakon zarginsa da yayi da soyayya da budurwarsa.

Bayan aukuwar lamarin a cibiyar kasuwanci ta Bunamubi, an hanzarta mika Watsosi zuwa wani asibiti sakamakon zubar da jinin da yakeyi ba kakkautawa.

Watsotsi dalibi ne a makarantar sakandire ta Bulucheke dake yankin Bududa kuma ya rasu ne a ranar Litinin. Har yanzu dai gawarsa tana ma'adanar gawawwaki a asibiti don gano sanadiyyar mutuwarsa.

DUBA WANNAN: Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce

Kwamandan 'yan sandan yankin Bududa Jaffar Magyezi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba kuma yace ana neman wanda ake zargin ido rufe.

"Muna neman dalibin wanda mahaifinsa ke boyesa bayan mutuwar dan makarantar," in ji shi.

Tashin hankali a yankin ya fara ne bayan da 'yan uwan mamacin suka yi yunkurin harar 'yan uwan wanda ake zargin don daukar fansa.

Amma kuma Magyezi ya bukaci 'yan uwan mamacin da su dau hakuri zuwa lokacin da za a kama wanda ake zargin a gurfanar dashi.

"Abin bakin ciki ne ya faru amma muna bukatar 'yan uwan mamacin da su guji yunkurin daukar fansa," in ji shugaban karamar hukumar Bunamubi.

"Abin mamaki ne a ce dan shekaru 10 na da budurwa wacce yake shirye da aikata komai don kariya gareta a wannan kananan shekarun," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel