Yadda akayi jina-jina, aka hana yan kwallon Kano Pillars fitowa daga fili a Katsina

Yadda akayi jina-jina, aka hana yan kwallon Kano Pillars fitowa daga fili a Katsina

Wasu matasa da ake kyautata zaton mabiyan kungiyar kwallon Katsina United ne sun tayar da zaune tsaye bayan wasan kwallonsu da Kano Pillars da aka karkare 1-1 kunnen jaki.

Duk da yawan jami'an tsaron dake tsare filin kwallon Muhammadu Dikko, yan tada zaune tsayen sun hana yan kwallon Kano Pillars fitowa daga filin har na tsawon sa'o'i da dama.

Daily Trust ta ruwaito cewa yayinda aka tafi hutun rabin lokaci, yan kwallon Kano Pillars sun gaza shiga dakin hutu saboda tsoron kada a kawo musu hari.

Abin ya kara muni bayan kammala wasan inda matasan Katsinan suka tare kofofin fita daga cikin filin kwallon.

DUBA NAN: Harin sarkin Potiskum: An kashe mutane 30, anyi awon gaba da 100

Sakamakon haka, sai aka fara fadace-fadace tsakanin mabiya Katsina United da Kano Pillars kuma an yi jina-jina.

Bayan sa'o'i da dama, jami'an tsaro sun samu fitar da yan kwallon Kano Pillars wajen gari.

Bisa ga rahoton jami'an tsaro, an tare hanyar Katsina zuwa Kano. Hakan ya tilasta yan Kano Pillars bin wata hanyar daban kafin su isa Kano cikin dare.

Kakakin kungiyar kwallon Kano Pillarsa, Malam Idris Malikawa yace: "Mun canza hanya saboda jami'an tsaro sun fada mana an tare hanyar da mukayi niyyar bi."

"Yanzu mun bi ta Daura zuwa Kazaure zuwa Kano. Abin kunya ne a ce duk da irin abubuwan da mukayi na yin wasa cikin lumana, irin haka na faruwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel