Gwamnan Borno ya yi umurnin dakatar da likita kan karkatar da magungunan asibiti

Gwamnan Borno ya yi umurnin dakatar da likita kan karkatar da magungunan asibiti

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya umurci mahukunta na asibitin jihar da ta dakatar da wani likita da aka zarga da karkatar da magunguna daga wajen siyar da magani na asibitin

- Umurnin ya zo ne a lokacin da Zulum ya kai ziyarar bazata asibitin Umaru Shehu da ke Maiduguri a ranar Laraba

- Ya kuma bukaci mahukuntan asibitin da su duba yiwuwar horar da ma’aikatan jinya 200 a ciki da wajen kasar domin cike gurbin da masu ritaya

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya umurci mahukunta na asibitin jihar da ta dakatar da wani likita da aka zarga da karkatar da magunguna daga wajen siyar da magani na asibitin.

Zulum, a lokacin da ya kai ziyarar bazata asibitin Umaru Shehu da ke Maiduguri a ranar Laraba, ya umurci babban daraktan likitocin asibitocin Borno, da ya dakatar da likitan.

“Ta yaya wani likita zai kasance da hannu a siyar da magunguna? Wannan ba zai zamu karbuwa ba a wajen mu. A bincike shi sannan a dakatar dashi,” in ji Zulum.

Ya kuma bukaci mahukuntan asibitin da su duba yiwuwar horar da ma’aikatan jinya 200 a ciki da wajen kasar domin cike gurbin da masu ritaya suka bari kimanin su 97.

Ya ba likitoci yan bautar kasa da ke asibitin hakuri kan rashin samun alawus dinsu tsawon watanni biyar.

KU KARANTA KUMA: Matar Adam A Zango tayi maganar da ta firgita mutane kan rashin lafiyar Zee Pretty

Ya yi bayanin cewa an samu jinkirin be saboda yunkurin gwamnati na kakkabe rashin gaskiya a tsarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel