Fadar shugaban kasa ta ce za ta binciki gwamnonin da suka yi ruf-da-ciki da kudaden kananan hukumomi

Fadar shugaban kasa ta ce za ta binciki gwamnonin da suka yi ruf-da-ciki da kudaden kananan hukumomi

- Fadar shugaban kasa ta gargadi gwamnonin da ke yin sama da fadi da kudaden kananan hukumomin jihohinsu

- Fadar shugaban kasar ta bukaci ofishin attoney janar na kasa ta cigaba da saka idanu kan wadannan gwamnonin

- Hadimin shugaban kasa kan harkokin Neja Delta, Ita Enang ya ce za a gurfanar da wadannan gwamnonin a kotu da zarar waadinsu ya kare

Fadar shugaban kasa ta yi gargadin cewa za ta gurfanar da gwamnonin da ke yin sama da fadi da kudaden kananan hukumominsu da zarar sun sauka daga mulki.

Daily Trust ta ruwaito cewa fadar shugaban kasar ta yi wannan gargadin ne a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, inda ta kara da cewa ga zarar waadin gwamnonin ya zo karshe kuma kariyar da doka ta basu ya gushe za a gurfanar da su a kotu.

A yayin yin gargadin, Ita Enang, babban mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin Neja Delta, ya bukaci akanta janar na tarayya da attoney janar na kasa su rika sanya idanu a kan yadda ake kashe kudaden da aka bawa jihohi. Ya ce dole ayi hakan don ceto kananan hukumomi.

DUBA WANNAN: Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida

Mai magana da yawun Enang, Edet Ekenyong Etuk, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce mai gidan nasa ya ce "Dukkan gwamnoni su sani cewa za su fuskanci sharia kamar yadda doka ta tanada da zarar kariyar da doka ta basu ya gushe."

Ya bayyana cewa sunkuru ya mamaye galibin hedkwatan kananan hukumomi da cibiyoyin lafiya inda maaikata suka dena zuwa aiki duk da cewa suna karbar albashi.

A watan Disamban 219, Legit.ng ta wallafa sunayen wasu tsaffin gwamnoni da ministoci a da a halin yanzu ke fuskantar bincike kan zargin aikata laifuka daban-daban.

Wasu daga cikinsu sun hada da Jolly Nyame na jihar Taraba, Rochas Okorocha na jihar Imo, Diezani Alison Madueke da ta jagoranci ma'aikatar man fetur yayin mulkin Goodluck Jonathan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel