Gwamnoni za su gana da Buhari bayan Minista ya haramta aikin Dakarun Amotekun

Gwamnoni za su gana da Buhari bayan Minista ya haramta aikin Dakarun Amotekun

Ana sa ran cewa Gwamnonin Kudu maso Yammacin Najeriya za su hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon nan.

Kamar yadda labari ya zo mana, batun Rundunar Amotekun da gwamnonin Kudu maso Yamma su ka kirkira ne zai jawo zaman.

Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan shari’a, Abubakar Malami, ta bayyana cewa Amotekun ba su da hurumin aiki a dokar kasa.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba a ja ta a jiki wajen kirkiro wadannan Dakaru da za su yi aikin tsaro a Kudancin kasar ba.

Ko da dai Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da Sufetan ‘Yan Sanda game da wannan kokari da su ke yi tun kafin yanzu.

KU KARANTA: Jami'an tsaro su na neman janye jikinsu daga aikin Amotekun

Gwamnoni za su gana da Buhari bayan Minista ya haramta aiki Dakarun Amotekun
Gwamnoni za su ajiye banbanci su gana da Buhari a fadar Shugaban kasa
Asali: UGC

Wani na-kusa da gwamnonin ya shaidawa ‘Yan jarida cewa kafin makon nan ya kare, shugaban kasa zai zauna da gwamnonin jihohin.

Akwai kishin-kishin din cewa wasu na kusa da shugaban kasa ba su gamsu da wannan tsari da gwamnonin Yarbawa su ka zo da shi ba.

Dalilin rashin gamsuwa da wannan tsari shi ne shakka cewa Yankin na faman yunkurin ganin an sake yi wa tsarin Najeriya garambawul.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya ce za su iya zuwa kotu idan lamarin ya faskara. Gwamnan Oyo dai ya yi tir da matsayar gwamnatin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel