Obasanjo da Makinde sun shiga ganawar sirri

Obasanjo da Makinde sun shiga ganawar sirri

- A ranar Laraba ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shiga ganawar sirri da gwamnan jihar Oyo

- Sun yi ganawar sirrin ne a 'pent-house' da ke dakin karatu na fadar shugaban kasa da ke Abeokuta

- Wannan ce ziyara kashi ta biyu da Gwamna Seyi Makinde ya kai wa tsohon shugaban kasa Obasanjo tun bayan hawan shi mulkin jihar

A ranar Laraba ne tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shiga ganawar sirri da Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, a Abeukuta, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Taron wanda aka yi shi a gidan Olusegun Obasanjo dake dakin karatu na fadar shugaban kasa, ya dau sa'o'i masu yawa.

Gwamnan ya isa taron ne wajen karfe 2:30 na yamma. Bayan musayar gaishe-gaishe tsakaninsu, sun shiga 'pent-house' inda suka fara taron da ya kaisu har yammaci.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya ce nasara ce ga mutanen Imo

Wannan ne ziyara ta biyu da Gwamna Makinde ya kai wa Obasanjo tun bayan da ya hau kujerar shugabancin jihar Oyo. Ziyarar farko itace wacce ya kai bayan an rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar Oyo.

Bayan wannan ganawar sirrin, tsohon shugaban kasar ya karba bakuncin gwamnan tare da tawagarsa inda suka ci abincin rana. Ya ki yin tsokaci a kan abinda suka zanta a wannan taron ko a lokacin da aka rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164