Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kaiwa sarkin Patiskum hari a Kaduna, an garzaya da shi asibiti

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kaiwa sarkin Patiskum hari a Kaduna, an garzaya da shi asibiti

Wasu yan bingida sun kaiwa mai martaba sarkin Patiskum, Alhaji Umaru Bubaram, inda suka kashe fadawansa uku a babban titin Kaduna zuwa Zariya.

An bayyana cewa Sarkin na kai ziyara masarautun Arewacin Najeriya ne cikin shirye-shiryen kaddamar sabon Masallacin Patiskum da aka shirya yi ranar 18 ga watan Juaniru, 2020.

Yana hanyarsa ta tafiya Zariya ne yan bindiga suka budewa motarsa wuta.

Harin ya faru ne misalin karfe biyun dare a kauyen Fandatio, kusa da Maraban Jos.

Ba'a sani ko Sarkin musamman sukayi kokarin kaiwa hari ba amma Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya shafi wasu matafiya daban.

Daya daga cikin makusantan sarkin, Sarkin Yamman Patiskum, Alhaji Gidado Ibrahim, ya tabbatar da labarin a asibitin Barau Dikko da aka garzaya da sarkin.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da labarin kuma yace zasu saki jawabi anjima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel