Kilu ta ja bau: Wani ya kashe miji a yayin da yake kokarin raba fada tsakanin ma'aurata

Kilu ta ja bau: Wani ya kashe miji a yayin da yake kokarin raba fada tsakanin ma'aurata

- Kotun majistare dake Ebuta Meta ta jihar Legas ta bukaci a cigaba da garkame mata wani mutum a kan laifin kisan kai

- Magidancin ya kashe budurwa mai suna Farojoye ne bayan ya buga mata tabarya a yayin da taje raba shi fada da matar shi

- Sifetan 'yan sandan wanda shi ya gabatar da karar yace lamarin ya auku ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2019 wajen karfe 8:30 na safe

Kotun majistare ta Ebuta Meta dake jihar Legas ta garkame wani mutum mai shekaru 27 mai suna Damilola Farojoye a kan zargin shi da ake da bugewa tare da kashe wata ma'aikaciyar kamfanin Honeywell mai suna Omokhogie Francis Ayogwokha.

Jaridar Within Nigeria ta gano cewa mamaciyar mai suna Omokhogie ta nemi raba fadan da wanda ake zargin yake da matar shi. A nan ne kuwa Farojoye ya make ta da tabarya wanda hakan ya jawo mutuwarta.

A yayin magana a kan lamarin, Sifeta Chinalu Uwadione, mai gabatar da karar ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2019 wajen karfe 8:30 na safe a filin Adidas, Tolu dake Ajegunle a jihar Legas.

KU KARANTA: Tashin hankali: Dan damfara ya kone budurwarsa kurmus kan zargin cin amana

Wanda ake zargin ya roki rangwame a kan laifin da ya aikata amma ba a saurare shi ba.

Alkalin kotun, Adeola Adedayo ta bukaci a adana mata wanda ake zargin a gidan gyaran hali dake Ikoyi kafin daraktan gurfanarwa na jihar ya bada shawara.

An dage sauraron shari'ar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: