Yadda 'yan uwan mara lafiya suka yi wa likita mace zigidir a Abuja

Yadda 'yan uwan mara lafiya suka yi wa likita mace zigidir a Abuja

'Yan uwan wata mata da ta mutu a asibiti da ke unguwar Maitama a Abuja sun yi wa likita mace duka har ta kai ga sun yi mata zigidir kamar yadda LIB ta ruwaito.

Da ya ke magana wurin taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, Shugaban kungiyar Likitoci (NMA) reshen Abuja, Ekpe Philips wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce abin ya faru ne yayin da likitan ke gudanar da aikin ta.

Ya ce 'yan uwan mara lafiyar sun yi wa likitan duka ne saboda ta ki amincewa a yi wa mara lafiyar karin jini duk da cewa ta yi musu bayanin babu bakatar ayi karin jinin.

Ya ce, "Ya ce wannan rashin lafiya ne da matar ta dade tana fama da shi kuma an bata dukkan kulawa da ya dace bisa dokar aikin likita. Sai dai abin bakin ciki mara lafiyar ba ta samu sauki ba kuma ta mutu."

"A lokacin da ake jinyarta, 'yan uwanta sun dage cewa sai anyi mata karin jini duk da cewa babu bukatar hakan don jininta ya wadatar kuma karin jinin ka iya haifar da wani matsalar."

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

Ya kara da cewa 'yan uwan mara lafiyar sun yi barazanar kashe likitan saboda kin amincewa ta aikata abinda suka ce duk da irin bayanin da ta yi musu.

"Sun ko cika burinsu ta hanyar cin zarafinta, suka yi mata zigidir da rana tsaka. Wannan abin takaici ne kuma ba zamu amince da shi ba."

Mr Philip ya ce cin zarafin likitoci yayin da suke kan aikinsu ya fara zama ruwan dare. Ya ce kungiyarsu ba za ta lamunci hakan ba. Ya ce an kama wanda ake zargi da aikata abin kuma za a kai shi kotu. Ya ce kungiyarsu za ta taimakawa likitar don ganin an bi mata hakinta.

Yayin da ya ke tausayawa iyalan wanda ta mutu, ya bukaci masu jinyar marasa lafiya su rika bin dokokin da suka dace wurin shigar da korafinsu game da likitoci a maimakon daukar doka a hannunsu.

Ya yi kira ga ministan Abuja, Muhammad Bello ya samar da isashen tsaro ga likitocin Abuja don kare rayukansu.

Dukkan yunkurin da aka yi don ji ta bakin wanda ake zargi ya ci tura. Asibitin ya ki bayar da lambobin lambar waya ko adireshin wanda ake zargin don ya saba wa dokar aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel