Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida

Kano: Da haramtattun kuri'u aka zabi Ganduje - Abba Gida-Gida

Yayin da ake cigaba da sauraron shari'ar daukaka karar kallubalantar zaben Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a ranar Talata, dan takarar jam'iyyar Peoples Democracy Party (PDP) a zaben Maris 9, 2019, Abba Kabiru-Yusuf ya bukaci kotun koli da bayyana shi a matsayin hallastacen zababben gwamnan jihar.

Abba-Yusuf ya ce duba da cewa shine ya samu kuri'u mafi rinjaye, shine dan takarar da ya cika tanadin sashi na 179 na dokar zabe.

Da ya ke jawabi kan daukaka kararsa, Adegboyega Awomolo (SAN), ya bukaci kotun kolin da ajiye hukuncin da kananan kotuna da - kotun zabe da kotun daukaka kara su kari a kan shari'ar na tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Awomolo ya ce baturen zabe na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a Kano ya sanar da sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris 2019 na kananan hukumomi 44 a jihar Kano kuma ya bayar da fom EC8D da ke dauke da takaitaccen kuri'un da aka sanar a rumfunan zabe 207.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

Ya ce kotun koli a wasu shari'ar da bayyana cewa saba doka ne baturen zabe ya soke sakamakon zaben kananan hukumomi bayan ya riga ya sanar.

Ya ce, "Bayyana cewa zabe bai kammalu ba (inconclusive) bayan soke sakamakon rumfunan zabe 207 lamari ne da ya fi karfin ikon baturen zabe."

Sai dai Ahmed Raji (SAN), Alex Izinyon (SAN) da Offiong Offiong (SAN) da ke wakiltan INEC, APC da Gwamna Ganduje kamar yadda aka jera sun bukaci kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar ta Kabiru Yusuf da PDP.

Raji ya ce babu wata hujja da ke nuna baturen zaben ya soke sakamakon zabe amma abinda ya ke a hukumance shine baturen zaben ya kasa tattara sakamakon zaben a ranar.

Ya ce, "Ina kira ga mai daraja ya yi watsi da wannan daukaka karar ya kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotunan suka bayan a baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel