Buhari ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya ce nasara ce ga mutanen Imo

Buhari ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya ce nasara ce ga mutanen Imo

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa kotun koli kan 'juriya da jarumtaka' na mayarwa Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, nasarar lashe zaben ranar 9 ga watan Maris na 2019 a Imo.

Shugaban kasar ya yi wannan yabon ne yayin da ya ke martani kan hukuncin da kotun koli ta yake na soke nasarar Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan da kuma sanar da cewa Uzodinma ne ya lashe zaben.

Buhari ya ce: "Hanyar neman adalci tana da tsawo da wahalar bi amma itace hanyar da ta fi dacewa ga duk wanda ya ke ganin an take masa hakkinsa.

"A karkashin wannan sabuwar gwamnatin, za a ga sabuwar tafiya ta inganta rayuwar mutanen Imo. Daga karshe, mutanen jihar Imo sun yi nasara."

Da ya ke taya sabon gwamnan murna, shugaban kasar ya bukaci Mr Uzodinma ya cigaba da yada akidojin APC kuma ya hada kan mutanen jihar ta hanyar janyo kowa a jiki a gwamnatinsa.

DUBA WANNAN: Layin waya: An maka diyar Buhari da DSS a kotu

Kotun kolin ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP ta kuma tabbatar da Hope Uzodinma, na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Babbar kotun, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) data karbe shahadar cin zabe daga hannun Ihedioha tare da mika shi ga Uzodinma ba tare da wani bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel