Daga gadon asibiti a Landan: Ina nan dawowa in yaki yan zagon kasa - Kauran Bauchi

Daga gadon asibiti a Landan: Ina nan dawowa in yaki yan zagon kasa - Kauran Bauchi

Yayinda yake sauraron shari'ar kotun koli kan zaben gwamnan jihar Bauchi, gwamna Bala Mohammed, wanda ke kwance a asibiti a birnin Landan ya turo wasika kan wasu masu shirya masa tuggu daga cikin gidansa.

Gwamnan ya ce yana nan dawowa yaki daga wasu yan cikin gwamnatinsa dake shirya masa kaidin fadi.

Gwamnan ya kyautata zaton samun nasara a kotun koli.

Mai magana da yawunsa, Mukhtari Gidado, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki cewa mai gidansa "zai dau mataki kan wasu yan zagon kasa kuma maras godiyan Allah cikin gidansa."

Ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabi na musamman da ya aikewa al'ummar jihar yayinda yake jinya a asibiti a Landan.

"Gwamnan yace wasu da ba'a tunani suna hada kai da abokan hamayya wajen ganin an ga bayan gwamnatin nan a kotun koli, yana tabbatar musu cewa zasu ji kunya."

"Ina asibiti a Landan amma mun yi imanin cewa Hasbunallahu. Shine wanda zai iya bamu nasara, insha Allahu zamu samu nasara."

Mun kawo muku rahoton cewa An kwantar da Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed a wani asibiti a London sakamakon wani ciwon da ba a bayyana ba.

A takardar da babban mataimakin gwamnan na musamman a bangaren yada labarai, Mukhtar Gidado ya mika ga manema labarai a jiya a Bauchi, ya bayyana sako na musamman ga jama'ar jihar daga gwamnan.

Ya sanar da cewa yana kwance a gadon asibiti a birnin London a yayin da kotun koli ke gab da jin daukaka karar da aka yi mai kalubalantar nasarar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel