Da duminsa: DSS ta gurfanar da wanda ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya Umar Farouq

Da duminsa: DSS ta gurfanar da wanda ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya Umar Farouq

Hukumar leken asiri na farin kaya DSS, a ranar Talata ta gurfanar da Kabiru Mohammed, wanda ya kirkiro bidiyon labarin karya na daurin auren shugaba Muhammadu Buhari da ministar walwala, Sadiya Umar Farouq.

Za ku tuna cewa hukumar DSS ta yi ram da Kabiru ne a shekarar 2019.

An gurfanar da shi gaban kotun Majistare na 72, unguwar Nomans Lan a jihar Kano.

An gurfanar da shi kan laifuka biyu na kokarin bata suna da kuma karya mai halakawa, kuma hakan ya sabawa sashe na 392 da 393 da dokar jihar Kano.

Idan aka tabbatar da laifi kan Kabiru Mohammed, za'a iya yanke masa hukunci daurin shekaru uku a gidan gyara hali.

Mun kawo muku a baya cewa Yayin bayyana matashin a hedkwatan hukumar dake Abuja, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa matashin ya amince da kirkiran bidiyon da rabawa kuma dan kungiyar Kwankwasiyya.

Peter Afunanya yace an kaddamar da bincike ne kan lamarin lokacin da ministar kudi, Zainab Shamsuna, ta shigar da kara.

Yace: "A shekarar 2019, tsakanin watan Agusta da Oktoba, wata bidiyon sharri ta bayyana a fadin Najeriya da ke nuna cewa shugaban kasa na shirin aure da daya daga cikin ministocinsa."

"Ta farko itace ministar Ilimi, Hajiya Zainab Ahmad sannan kuma ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Farouq."

"Sunansa Kabiru Mohammed. Dan asalin jihar Kano ne, Yana da shekaru 32. Yayi karatun difloma a ilmin Hausa da Fulfulde a kwalejin ilimin tarayya ta Kano."

"Ya tona asirin kansa kuma bincike ya nuna dukkan yadda suka hada bidiyoyin da yadawa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel