Yanzu-yanzu: Surukin Okorocha ya hakura da kujerar gwamna, ya janye kara a kotun koli

Yanzu-yanzu: Surukin Okorocha ya hakura da kujerar gwamna, ya janye kara a kotun koli

- Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Action Alliance (AA) a zaben 9 ga wata Maris a jihar Imo ya janye daukaka kara

- Lauyan Uche Nwosu ya ce ya yanke hukuncin rungumar hukuncin kotun kolin na ranar 20 ga watan Disamba 2019

- A don haka ne kungiyar alkalai 7 din ta kotun tayi watsi da wannan karar gani cewa mai daukaka ta ya janye

Dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar AA a zaben ranar 9 ga watan Maris na 2019 a jihar Imo, Uche Nwosu, ya janye daukaka karar da yayi na kalubalantar nasarar Gwamna Emeka Ihedioha.

Lauyansa, Solomon Umoh (SAN), ya sanar da kungiyar alkalan na kotun kolin wadanda suka sami jagorancin alkalin alkalai, Mai sharia Tanko Muhammad, cewa wannan hukuncin janye daukaka karar ya biyo bayan hukuncin kotun koli ne na ranar 20 ga watan Disamba na 2019.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

A yayin sanar da janye daukaka karar a ranar Talata, Umohu yace: “Duba da hukuncin wannan kotun mai lamba 1384/2019 wanda aka yi a ranar 20 ga watan Disamba na 2019 tare da shawarata ga wanda nake karewa, mun yanke hukuncin janye daukaka kara.”

A yayin mayar da martanin lauyan Gwamna Emeka Ihedioha wanda ya lashe zaben a karkashin jam’iyyar PDP, ya yi kira ga kotun da tayi watsi da wannan karar ganin cewa mai daukaka karar ya janye.

Alkalan ba ja-in-ja su ka yi watsi da wannan daukaka karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel