Yanzu-yanzu: Kotun koli ta dage shari'ar Ganduje da Abba Gida-Gida

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta dage shari'ar Ganduje da Abba Gida-Gida

Karo na uku, Kotun kolin Najeriya ta dage shari;ar zaben gwamnan jihar Kano zuwa ranar Litinin, 20 ga watan Junairu, 2020.

Kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin babban Alkalan tarayya, Jastis Tanko Muhammad, ya yanke shawarar dage karar ne saboda bukatun lauyoyin Ganduje da lauyoyin Abba Gida-Gida suka gabatar.

Wadanda suka shigar da kara kotun koli sune Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa, Peoples Democratic Party (PDP).

Wadanda aka kai karan sune hukumar gudanar da zabe INEC, jam'iyyar All Progressives Congress APC da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Zaku tuna cewa a jiya CJN Tanko Muhammad, ya dakatad da shari'ar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, sakamakon rashin lafiyan daya daga cikin Alkalan.

A yau, an maye Alkalin dake rashin lafiya, John Okonkwo da Amina Augie.

Sauran Alkalan sune Sylvester Ngwuta, Olukayode Ariwoola, Kudirat Kekere-Ekun, Amiru Sanusi da Uwani Abba-Aji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel