Alkalan kotun koli sun hallara domin gabatar da shari'ar zaben gwamnoni 7

Alkalan kotun koli sun hallara domin gabatar da shari'ar zaben gwamnoni 7

Alkalan Kotun kolin Najeriya bakwai sun hallara domin cigaba da sauraron kara da yanke hukunci na karshe kan zaben gwamnoni bakwai a yau.

A jiya Litini, shugaban Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad, ya dakatad da shari'ar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, na jihar Sokoto, da sauran jihohi shida zuwa ranar Talata.

Alkali Tanko Muhammad ya dawo cikin kotun bayan ya fita da farko sakamakon hayaniya da cinkoson mabiyan yan siyasan da suka cika kotun.

Daga baya kuma ya dakatad da zaman gaba daya sakamakon rashin lafiyar daya daga cikin Alkalan bakwai.

Jastis Muhammad Tanko bai ambaci Alkalin dake fama da rashin lafiyan ba.

Ga jerin shari'un da za'a yanke gobe:

1. Kano: Tsakanin Ganduje (APC) da Abba GIda-Gida (PDP)

2. Sokoto: Tsakanin Aminu Waziri Tambuwal (PDP) da Ahmad Aliyu Sokoto (APC)

3. Imo: Emeka Ihedioha (PDP) da Hope Uzodinma (APC)

4. Bauchi: Bala Mohammed (PDP) da Mohammaed Abubakar (APC)

5. Benue: Samuel Ortom (PDP) da Emmanuel Jime (APC)

6. Plateau: Simon Lalong (APC) da Jeremiah Useni (PDP)

7. Adamawa: Ahmadu Fintiri (PDP) da Bindow Jibrilla (APC)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel