Rainin wayo: Yadda aka daura min da gardi a zuwan Mace - Sheikh Mohammed Mutumba

Rainin wayo: Yadda aka daura min da gardi a zuwan Mace - Sheikh Mohammed Mutumba

Sheikh Mohammed Mutumba babban limamin masallacin Kyampisi ne dake Uganda wanda ya gano amaryarsa katon gardi ce. Ma'auratan basu taba kwanciyar aure ba kuma sunyi makonni biyu da aure amma amaryar tace tana jinin al'ada ne.

Mutumba yace, bayan matarsa tayi ikirarin cewa tana jinin al'ada, ya hakura tare da jiran har jinin ya dauke.

Amma kuma sa'ar Nabukeera ta kare ne bayan makwabcin Mutumba yayi ikirarin cewa sabuwar amaryar Mutumba ta tsallake katanga tare da satar masa talabijin da kayan sanyawa.

Mutumba ya karba hayar gida mai dakuna biyu wanda suka tare da amarya Nabukeera. Amma kuma katangar da ta raba gidajen hayan biyu bata kai kwanon rufi ba.

Makwabcin ya kai wa 'yan sandan yankin Kayunga kara wanda hakan yasa aka kama Nabukeera.

Babban jami'i mai bincike a ofishin 'yan sandan yankin Kayunga, Isaac Mugera yace Nabukeera amarya ta isa ofishin 'yan sandan ne sanye da katon hijab da takalman mata.

"Kamar yadda 'yan sanda suka saba, jami'a mace zata caje wanda ake zargin kafin ta tura ta bayan kanta. Abin mamakin ya fara ne da jami'ar ta gano cewa namiji ne ya tura kaya a rigar nono wadanda suka tashi kamar na gaske." Mugera ya sanar da wata jaridar yankin.

"Bayan cigaba da bincike, mun gano cewa wanda ake zargin tana da mazakuta. Tuni muka sanar da mijinta wanda ya rakota har ofishin 'yan sandan," ya ce.

Kamar yadda Daily Monitor ta sanar, wannan labari ya matukar girgiza Mutumba wanda ya bukaci a bashi damar ganin jikin matarsa na maza.

Bayan dubawa da limamin yayi, ya zargi Nabukeera da zama barawo.

"Ina neman matar aure a lokacin. Da naci karo da kyakyawar yarinya sanye da hijab, sai na bukaci ta aureni kuma ta amince. Munyi soyayya amma tace ba zamu fara komai ba sai na kai sadakinta kuma an daura aurenmu," Mutumba ya ce.

Mugera yace daga baya Nabukeera ta bayyana cewa ita dai gardi ce kuma sunanta Richard Tumushabe mai shekaru 27.

Tuni aka mika lamarin ga babban alkalin garin don gurfanarwa tare da yanke hukuncin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel