Alkali ya daure Akantan coci a gidan yari bayan ya yi gaba da kudin sadaka
Babban kotun tarayya da ke zama a Garin Yola a jihar Adamawa ya samu wani Ibrahim Aku da laifin satar kudin Bayin Allah.
Kamar yadda mu ka samu labari Alkali Nathan Musa ya samu Mista Ibrahim Aku da laifin satar kudin sadaka da aka tara a coci.
EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ce ta shigar da karar Aku a gaban kuliya da laifin sata da sauransu.
Alkali mai shari’a ya ba hukumar EFCC gaskiya a shari’ar, inda ya gamsu cewa Aku ya yi amfani da sunan coci ya karbi kudin Mabiya.
KU KARANTA: Saurayi ya dauki bidiyo bayan ya yi wa Budurwa fyade
Aku wanda Akawu ne a cocin, ya amsa laifinsa da kansa, wanda hakan ya sa Alkali ya lafta masa daurin shekara 18 a gidan kurkuku.
Alkalin ya hana wannan mutumi da ya ci Naira miliyan 15.5 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018 da sunan cocin damar biyan tara.
Bayan haka Alkali ya umarci wannan Mai laifi ya maido duk abin da ya karba, wanda a karshe za a tattarasu a maidawa coci.
Bayan shari’ar, wani jami’in EFCC ya ce: “An damkawa mai laifin amanar kudin coci, amma ya sace kudin, ya buga takardun bogi.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng