Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi

Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi

- Shafin babban faston Najeriya, TB Joshua ya wallafa labarin yadda aka gano wani mutum bayan shekaru 12 da bacewa

- Mutumin ya koma daji ne rayuwa da birai tare da dogara da 'ya'yan itace da kuma ganyayyaki don rayuwa

- Amfani da ruwan waraka da 'yar uwar shi tayi ne ya jawo mutumin zuwa gefen titi har ta gan shi

Shafin babban fasto TB Joshua na kafar sada zumuntar Facebook ya wallafa wani labari mai matukar bada tausayi.

Kamar yadda aka wallafa, wani mutum ne ya bace na shekaru goma sha biyu amma da taimakon 'ruwan waraka' aka gano shi. Ayamu dan asalin kasar Zimbabwe ya bar gida ne da niyyar tafiya kasar Afirka ta kudu ba tare da albarkar iyayen shi ba. Hakazalika ya gudu inda ya bar matar shi da bata dade da haihuwa ba. Cikin rashin sa'a kuwa Ayamu ya haukace inda ya koma rayuwa a daji tare da birai kuma ya dogara a kan 'ya'yan itace da ganyayyaki don rayuwa.

Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi
Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi
Asali: Facebook

Bayan kanwar Ayamu ta halarci cocin fasto TB Joshua, sai aka bata wannan 'ruwan waraka' inda daga fitarta taci karo da Ayamu a gefen titi. Bayan nan ne ta kaishi gaban fasto inda a take yayi wanka tare da shan wannan ruwan. A take ya kwanta baccin da yayi sa'o'i shida yana yi.

KU KARANTA: Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda kawai yana so ya burge abokanan shi

Bayan tashin shi ne ya karba Yesu a rayuwar shi kuma ya tuna da 'yan uwan shi. A nan ya bayyana nadamar shi tare da barin duk rayuwa mara amfani da yayi a da. Ya bukaci yafiyar iyayen shi tare da bayyana cewa ana cin zarafin shi a dajin. Don wata rana ya kan tashi ya ga jikin shi da maniyyin namiji.

Har yanzu dai, babbar cocin TB Joshua dake Legas ce ta fi kowacce coci jan hankalin jama'a, irin wadannan mu'ujizojin ne ke jan hankulan mutane kala-kala.

Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi
Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel