Wanene sabon Kocin kungiyar Barcelona Enrique 'Quique' Setién Solar

Wanene sabon Kocin kungiyar Barcelona Enrique 'Quique' Setién Solar

Yayin da labari ya gama shiga ko ina cewa Barcelona ta sallami Ernesto Velverde daga matsayin koci, mun kawo takaitaccen tarihin sabon kocin da aka nada.

Enrique 'Quique' Setién Solar shi ne zai ja ragamar kungiyar wajen horas da ‘Yan wasan ta. Ana sa ran cewa Quique zai shafe shekaru akalla biyu da kungiyar.

Setién wanda ake yi wa lakabi da 'El Maestro' tun a gida ya na cikin Yaran Marigayi Johan Cruyff a kwallo. Shin wanene wannan sabon koci da aka yi haya jiya?

1. Wanene Enrique Setién Solar

An haifi sabon Mai horas da kungiyar Kataloniyar ne a Ranar 27 ga Watan Satumban 1958. Hakan na nufin shekarun Enrique Solar ya na da shekaru 61 da haihuwa. Ainihinsa da ‘Dan kasar Sifen ne.

KU KARANTA: Aliko Dangote ya na nan a kan batun sayen kungiyar Arsenal

Wanene sabon Kocin kungiyar Barcelona Enrique 'Quique' Setién Solar
Kungiyar Barcelona Enrique ta sallami Velverde bayan Atletico ta doke ta
Asali: Getty Images

2. ‘Dan wasa

A lokacin da Kocin ya ke taka leda ya bugawa kulob din gida sa’ilin da ya ke kuruciyarsa. Daga cikinsu akwai Real Racing Club, Atlético Madrid, Logroñés, da kuma kungiyar Levante.

Enrique Solar ya fara kwallo ne a kan turbaya kafin ya shiga kwallon kafa. Solar ya kuma bugawa kasar Sifen kwallo a matsayin ‘Dan wasan tsakiya, sai dai bai yi wani fice a zamanin na sa ba.

3. Horaswa

Kafin zuwansa Barcelona, Kocin ya yi aiki da kungiyarsa ta Real Racing Club, Poli Ejido, Logroñés, Lugo, Las Palmas, Real Betis. Kocin ya kuma taba aiki da kuma kasar Equatorial Guinea.

A 2018 kocin ya je har gida ya doke Barcelona. A bara ma Real Madrid da Atletico sun sha kashi a hannunsa. Ana sa ran za a ga kyakkyawan kwallo dalla-dalla a wajen sabon Mai horaswan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel