Layin waya: An maka diyar Buhari da DSS a kotu

Layin waya: An maka diyar Buhari da DSS a kotu

Wani dan kasuwa mai suna Anthony Okolie ya shiga hannun jami'an 'yan sandan farin kaya inda ya kwashe makonni goma. Tuni kuwa ya maka su kotu tare da bukatar diyyar naira miliyan 500.

A karar da Okolie ya shigar a babbar kotun tarayya dake Asaba ta hannun lauyansa Tope Akinyode, ya bukaci naira miliyan 500 daga hannun Hanan Buhari, autar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma kamfanin sadarwa na MTN, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Karar mai lamba FHC/ASB/CS/3/2020 na bukatar DSS, Hanan da kamfanin MTN da su biya diyyar naira miliyan 500 a matsayin kudin danne masa hakkokinsa da suka yi.

A wata takardar shaida mai goyon bayan karar, an kama shi ne a ranar 19 ga watan Yuli, 2019 a Asaba jihar Delta, saboda amfani da wani layi da Hanan ta taba amfani dashi.

Kamar yadda yace, ya kwashi makonni 10 a daure a hannun DSS yana jiran Hanan wacce take karatu a London, kafin ta dawo gida.

Okolie yace ya hado da shaidar siyan layin wayar a karar.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

Takardar tace, "a ranar 8 ga watan Disamba 2029, a kasuwar Ogbeogonogo dake kan titin Nabu a Asaba na siya Layin waya mai lambobi 09035666662 a kan kudi N1,000 kuma an bani harda gidan layin a matsayin shaidar siyayyar,"

"Kamar yadda dokar sadarwa ta Najeriya ta tanadar, na karasa wajen wani mai suna Jeff wanda yayi min rijistar layin da sunana. A watan Yuli ne wani abokin kasuwanci na a Asaba ya shiga hannun DSS. Daga nan suka tambaye shi da wa yayi magana ta karshe, yace ni ne. Daga nan suka kamani har zuwa babban ofishinsu dake Asaba. Sun bayyana min cewa fadar shugaban kasa ce ta umarcesu da kama ni kuma zasu kaini Abuja don cigaba da bincike." in ji takardar

Mai karar ya ce yayi wa DSS din bayanin yadda ya samu layin wayar, amma sai aka ce masa Hanan Buhari ta taba amfani dashi.

"Sun ce banda gaskiya ta yadda nayi amfani da layin wayar da Hanan tayi amfani da shi."

Okolie ya zargi cewa an hana shi zantawa da lauyansa ko bayan da aka garkameshi.

Dan kasuwar yayi ikirarin cewa har mahaifiyarsa ba a bari ta ganshi ba kuma hakan yasa mata hawan jini. Ya rasa N5m a kasuwancinsa na tsawon lokacin da yake kulle.

Ya kara da cewa, "an garkameni na tsawon kwanaki ba tare da an samu Hanan tayi magana a kan hakan ba. Tace tana fama da karatu a London."

Ya bukaci kotun da ta bayyana cewa take hakkin dan Adam ne garkamesa da aka yi. Hakan kuwa yaci karo da sashi na 35 da 34 na kundin tsarin mulki na 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel