Buhari ya zabi wasu amintattu da zasu sanya idanu don ganin an aiwatar da aikin wutar Mambilla

Buhari ya zabi wasu amintattu da zasu sanya idanu don ganin an aiwatar da aikin wutar Mambilla

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wasu kwamitoci guda biyu da zasu sanya idanu wajen gudanar da aikin samar da wutar Mamabilla na Megawatta 3050 a jahar Taraba, yankin Arewa ta tsakiya.

Kwamitocin guda biyu sun hada da kwamitin ministoci da zasu dinga tattaunawa tare da auna matsayin aikin a karkashin jagorancin ministan wutar lantarki, da kuma kwamitin tabbatar da an gudanar da aikin yadda ya kamata tare da kammala shi a lokacin daya dace.

KU KARANTA: Barawo ya diro daga gidan sama mai hawa 2, ya karya wuya a jahar Imo

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito shi wannan kwamiti na biyu an kafa shi ne a karkashin jagorancin darakta a ma’aikatar wutar lantarki, Injiniya Faruk Yusuf, wanda zai mika rahotonsa ga minista ta hannun babban sakataren ma’aikatar, Didi Walson-Jack.

Cikin wani rahoto da majiyar Legit.ng ta yi a kwanakin baya bayan ta tattauna da ministan lantarki, Mamman Saleh, ta ruwaito ministan yace sai yanzu aka fara aikin Mambilla, sakamakon babu abin da aka yi game da aikin har sai da ya zo.

Tsawon shekaru 40 kenan ake ta kokarin samar da wutar Mambilla, wanda da farko an tsara shi ne a kan zai samar da 2600MW, amma aikin ya yi ta fama da matsaloli irin na sharia tun a shekarar 2003 zuwa 2014.

Da wannan cigaba da aka samu, ana sa ran aikin wutar Mambilla zai fara ganga ganga, kuma yan Najeriya suna sa ran idan har aikin ya kammala, za’a samu karin wutar lantarki a Najeriya, sai dai abin tambayar shi ne kamfanonin wutar lantarki da aka sayar zasu iya raba wutar ga jama’a.?

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel