Dakatar da yanke hukuncin shari'ar zaben gwamna a jihohi 7: Abubuwa 3 da suka faru a kotun Koli

Dakatar da yanke hukuncin shari'ar zaben gwamna a jihohi 7: Abubuwa 3 da suka faru a kotun Koli

A ranar Litinin ne babban alkalin alkalai na kasa (CJN), Jastis Tanko Muhammad, ya jagoranci zaman kotun koli domin yanke hukunci a sauran jihohi 7 da har yanzu ba kammala shari'ar kujerar gwamnoninsu ba.

Kotun ta zauna ne domin yanke hukunci a kan karar zaben kujerun gwamnonin jihohin Kano, Imo, Bauchi, Benue, Plateu, Sokoto da Adamawa.

Sai dai, kotun kolin ta gaza yanke hukuncin a ranar Litinin tare da daga zamanta zuwa ranar Talata, 14 ga watan Janairu.

Ga abubuwa uku da suka tilasta kotun daga zamanta;

1. Hargitsi da hayaniya sun tilasta wa CJN ficewa daga zauren kotu ba shiri

Babban alkalin Najeriya, Jastis Tanko Muhammad ya fice daga zauren kotu babu shiri sakamakon hargitsi da hayaniya da ta cika babban zauren kotun koli.

Daraktan shari'a na kotun kolin, Ibrahim Gold ya umarci jama'ar da ba wani takamaiman lamari ya shigo dasu kotun ba da su fice daga zauren kotun.

Ya kara da cewa manyan lauyoyin bangarori da kuma wasu mutane hudu kacal aka amince da su zauna a zauren kotun. "Idan ka shigo ba matsayin lauyan mai kara bane ko wanda ake kara, muna rokonka da ka bar zauren kotun," in ji shi.

2. Babban alkalin kotun da ba a bayyana sunansa ya gamu da rashin lafiya

Bayan al'amura sun dan lafa kuma ya koma kan kujerarsa ya zauna, Jastis Muhammad ya gaggauta sanar da cewa an dakatar da sauraro da kuma yanke hukunci a kan kararrakin zabe saboda rashin lafiyar da ta fada wa daya daga cikin alkalan kotun guda bakwai.

Alkalin alkalan ya bayyana cewa an daga dukkan kararrakin zuwa ranar Talata domin a duba lafiyar alkalin da ba a bayyana sunansa ba.

3. Jifan tsohon gwamnan Bauchi

Bayan an daga zaman kotun, tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya sha ruwan jifa yayin da ya fito daga zauren kotun.

Tsohon gwamnan ya sha jifa ne da robobin ruwan sha yayin da yake daga hannayensa tare da yin alamar "4+4".

Hatta a lokacin da jami'an tsaro ke kokarin cetonsa, masu jifansa basu daina fadin "karya ne!" "Barawo" ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng