Jamilu Gwamna, jigo a APC, ya dauki nauyin karatun matasa 10 a jami'ar kasar waje

Jamilu Gwamna, jigo a APC, ya dauki nauyin karatun matasa 10 a jami'ar kasar waje

Manajan darektan kamfanin raba hasken wutar lantarki a shiyyar Kano, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya dauki nauyin karatun matasa 10 'yan asalin jihar Gombe a wasu jami'o'in kasar Morocco.

Gwamna ya zabi matasan, wadanda yawancinsu marasa karfi ne, domin basu tallafin yin karatu a wasu manyan jami'o'i guda biyu dake kasar Morocco.

Da yake magana amadadin iyayen yaran da aka dauki nauyinsu, Alhaji Yakubu Adamu, ya jinjina wa Gwamna tare da yaba wa namijin kokarin da ya yi wajen kafa sabon tarihi a jihar Gombe.

"Bani da wata alaka da Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, haka suma iyayen yaran da ya tallafa wa basu da wata alaka da shi. Amma saboda halinsa na kirki, ya dauki nauyin yara, 'ya'yan talaka wa, domin su je har kasar Morocco su yo karatun jami'a. Ya dauke musu nauyin komai, har ciyar wa da sauransu," a cewar Adamu, dan asalin karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe.

Jamilu Gwamna, jigo a APC, ya dauki nauyin karatun matasa 10 a jami'ar kasar waje
Jamilu Gwamna
Asali: Depositphotos

Kazalika, Sani Abubakar Banki, mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Gombe, ya jinjina wa Gwamna tare da bayyana cewa ya dade yana taimakon jama'a daban - daban ba tare da la'akari da wurin da suka fito ba.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun kashe alkalin kungiyar Boko Haram da wasu manyan kwamandoji

Matasan da suka samu tallafin sun hada da Hassan Adamu Dashi daga karamar hukumar Dukku, Abdulhadi Auwal Ishiaku daga karamar hukumar Gombe, Abdulmumini Kabir Talasse daga karamar hukumar Balanga, wadanda zasu yi karatu a jami'ar Mohammed Khamis dake birnin Rabat a kasar Morocco.

Ragowar sune; Kabiru Muhammad Malam Sidi daga karamar hukumar Kwami, Talatu Tanimu daga karamar hukumar Kaltungo, Ahmad Adamu Umar Kumo Daga karamar hukumar Akko, Solomon Musa Kalmai daga karamar hukumar Billiri, Abdullahi Abubakar Kashere daga Akko, Muhammad Adamu daga karamar hukumar Funakaye da Nazif Yakubu Adamu Dadinkowa daga karamar hukumar Yamatu Deba. Zasu yi karatu ne a jami'ar Sidi Muhammad Bin Abdallah dake birnin Fes.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel