Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan dokar kara kudin haraji

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan dokar kara kudin haraji

- Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan gyararren dokar kudi

- Shugaba Buhari ya yi bayanin cewa dokar za ta yan Najeriya biyan kudin haraji kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi

- A cewar Buhari, dokar za ta janyo hankalin masu sanya hannun jari da kuma karawa gwamnati kudin shiga

A yau Litinin, 13 ga watan Junairu, 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar kudi.

Za ku tuna cewa shugaba Buhari ya aika dokar majalisar dokokin tarayya a shekarar 2019 a ranar da ya gabatar da kasafin kudin 2020.

Legit.ng ta kawo maku abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan doka da Buhari ya rattaba hannu:

1. Bankuna za su bukaci lambar haraji ta TIN kafin su budewa mutum sabon asusu.

2. Masu amfani da akawun a banki za su bukaci TIN kafin su iya cigaba da amfani da bankinsu.

3. Bankuna za su rika amfani da sakonnin gizo na E-mail wajen tuntubar hukumomin haraji.

4. Za a cire kamfanonin da ba su samun abin da ya kai Naira miliyan 25 a shekara daga jerin wadanda ake karbar haraji a hannunsu.

5. Za a zaftare kason harajin da ake karba daga hannun kamfanoni masu matsakaicin karfi wanda dukiyar juyarsu ke tsakanin miliyan 25 zuwa miliyan 100.

6. Dakatar da maimen karbar haraji (ma’ana karbar kudin haraji fiye da sau guda daga kamfani daya.)

7. Kawo karshen matsalolin da ake samu lokacin fara biyan harajin farko.

8. Sauya mafi karancin abin da za a karba a matsayin harajin zuwa 0.5% na uwar kudi. Wannan tsari zai yi tasiri ne ga wadanda ba su ba miliyan 25 baya ba.

9. Kamfanonin inshora za su iya dage biyan harajin asara zuwa wani lokaci.

10. An yi fatali da tsarin mafi karancin kaso na haraji ga kamfanonin inshora.

KU KARANTA: Kudirin haraji na Shugaba Buhari ya samu shiga a Majalisa

11. Kyautar garabasa 2% na kudin harajin da ke kan wuyan kananan kamfanoni da kuma garabasar 1% ga kamfanoni masu matsakaicin karfin da su ka biya harajinsu a lokacin fari.

12. Kawo sabon tsari ga Bakin da ke Najeriya su ke shigo da kaya daga kasashen waje.

13. Kara yawan harajin da ke hannun jarin kayan man fetur.

14. Wasu kadarori bayan filaye sun shiga cikin sahun dukiyoyin da ake la’akari da su.

15. Shigo da kudin harajin masarufi na VAT ga kayan da aka shigo da su Najeriya.

16. Za a kawo sabon tsari na kafe adadin kudin rajistar VAT a matsayin miliyan 25 a shekara.

17. Za a janye harajin hatimi da ake karba a kan kudin da ba su haura N10, 000 ba.

18. Za a janye karbar haraji idan mutum ya zuba kudi a cikin asusunsa.

19. Dakatar da wanda ya rasa aikin da bai kai Naira miliyan goma ba daga tsarin CGT.

20. Za a rika biyan VAT da ainihin takardun kudi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel