Daurin gindi: Aisha Buhari ta daura bidiyon Hanan cikin jirgin shugaban kasa duk da korafin yan Najeriya

Daurin gindi: Aisha Buhari ta daura bidiyon Hanan cikin jirgin shugaban kasa duk da korafin yan Najeriya

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta daura bidiyon diyarta, Hanan Buhari, cikin jirgin shugaban kasa inda ta tafi yawon ganin ido ciki.

Bidiyon na kusan minti daya ya nuna yadda Hanan ta yi yawon daukan hoton al'adun jihar Bauchi.

Hanan ta yi amfani da daya daga cikin jiragen shugaban kasa domin zuwa jihar Bauchi kuma hakan ya janyo cece-kuce inda yan Najeriya ke sukan Buhari da barin suna amfani da kudin al'umma wajen shagalinsu.

Babban lauya, Femi Falana, ya ce bai hallata ba a doka diyar shugaban kasa tayi amfani da jirgin shugaban kasa wajen harkan gabanta.

Amma duk da hakan, uwargidar shugaba Buhari, Aisha, ta daura bidiyon diyarta cikin jirgin da kuma abubuwan da taje yi jihar Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel