An kwantar da Gwamnan Bauchi a asibitin London saboda rashin lafiya

An kwantar da Gwamnan Bauchi a asibitin London saboda rashin lafiya

An kwantar da Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed a wani asibiti a London sakamakon wani ciwon da ba a bayyana ba.

A takardar da babban mataimakin gwamnan na musamman a bangaren yada labarai, Mukhtar Gidado ya mika ga manema labarai a jiya a Bauchi, ya bayyana sako na musamman ga jama'ar jihar daga gwamnan.

Ya sanar da cewa yana kwance a gadon asibiti a birnin London a yayin da kotun koli ke gab da jin daukaka karar da aka yi mai kalubalantar nasarar sa.

Takardar tace, "Ina kwance a gadon asibiti a London amma ina da tabbacin Allah ya isar mana kuma zai bamu nasara. Ina miko muku gaisuwa kuma nasara tamu ce da izinin Allah. Gaisuwa gareku duka."

Takardar ta kara jaddada cewa mulkin a shirye yake don kawo cigaba ga jihar Bauchi tare da tabbatar da adalci.

Ya kara da tabbatar da cewa zai duba tare da tabbatar da an saka wa duk wanda ya nuna jajircewarsa tare da tabbatar da ayyukan cigaban jihar Bauchi.

Kamar yadda yace, wannan lokacin da kotun kolin zata zartar da hukunci na karshe, shine lokacin da Ubangiji ya nuna mishi magoya bayansa na hakika.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga wadanda ya kira da 'magoya baya masu kishin kasa'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng