Ba zan taba kula ‘Yan hayaniyan da ba su zabe a Jihar Kaduna – Gwamna El-Rufai

Ba zan taba kula ‘Yan hayaniyan da ba su zabe a Jihar Kaduna – Gwamna El-Rufai

A jiya Lahadi, 12 ga Watan Junairun 2020 ne mu ka samu rahoto cewa an yi wata ‘yar takaddama tsakanin Nasir El-Rufai da Aisha Yesufu a dandalin Tuwita.

Rikicin ya fara ne bayan da Aisha Yesufu wanda ta na cikin manyan tafiyar BBOG ta taso gwamnan a gaba a kan wasu batutuwa da su ke tasowa a kasa.

Yesufu ta soki gwamna El-Rufai kan kin yin abin da ya dace wajen ceto wasu da aka yi garkuwa da su da kuma gano wadanda su ka kashe wani Soja a Kaduna.

Bayan haka, Aisha Yesufu ta hurowa gwamnan wuta game da wasu rubutu da ya yi a baya a kan yadda Iyalan Jonathan su ka rika amfani da jirgin shugaban kasa.

A lokacin Malam Nasir El-Rufai ya jam’iyyar hamayya, ya yi tir da yadda Mai dakin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ta ke hawa jirgin fadar shugaban kasar.

KU KARANTA: An binciko laifin wanda aka kama da tsohuwar lambar Hannan Buhari

An tado da wannan magana ne bayan da aka samu labarin cewa ‘Diyar shugaban kasa, Hannan Buhari, ta hau jirgin shugaban kasa, wanda ya jawo surutu.

Da aka taso gwamnan na APC a gaba, sai ya fito ya na maida martani ba tare da ya kama suna ba, ya na cewa, ba zai biyewa wasu mutane marasa aikin yi ba.

El-Rufai ya ce: “Wannan ya zama na farko kuma na karshe, ba na maida amsa a shafina ga kowane shashasha wanda bai taba zabe a jihar Kaduna ba.”

“Ina kokarin mulkin jihar mu ne ba tare da damuwa da wani Mai neman suna da sharara da ba a sanshi ba, maras aikin yin da bai da takardu ko adireshi.”

Daga baya gwamnan ya nuna cewa ba zai tanka su ba, amma zai yafewa duk masu yi masa sharri, inda ita kuma Yesufu ta cigaba da tofa albarkacin bakinta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel