Gobe kotun koli zata raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Gobe kotun koli zata raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na jam'iyyar APC da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, na PDP sun bayyana yadda suke kyautata zaton samun nasara a kotun kolin da za'a zauna gobe Litinin, 13 ga watan Junairu, 2020.

A ranar Juma'a, kotun kolin tarayya ta sanar da bangarorin biyu cewa ta zabi ranar Litinin domin yanke hukunci kan karar Abba Kabir Yusuf, inda yake kalubalantar nasarar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a zaben 9 da Maris, 2019.

Dan takarar PDP ya garzaya kotun koli ne bayan ya sha kasa hannun Ganduje a kotun zabe da kotun daukaka kara

Tsokaci kan shirye-shiryen zuwa kotun gobe, Ganduje ya bayyana cewa suna kyautata zaton samun nasara.

Gwamnan wanda yayi magana ta bakin kwamishanan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya ce suna kyautata zaton samun nasara kamar yadda suka samu a kotun zabe da kotun daukaka kara.

Yace: "In shaa Allah kotun koli za ta tabbatar da hukuncin kotun zabe da na daukaka kara."

A bangaren yan jam'iyyar PDP, Abba Gida-Gida, ya na kyautata zaton kotu zata bashi nasara.

Abba wanda yayi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, yace: "A matsayinmu na masu shigar da kara, muna kyautata zaton cewa kotun koli zata yanke hukunci cikin adalci da gaskiya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel