Ajali: Ladan ya mutu a cikin Masallaci yayin jiran lokacin kiran Sallar Asuba

Ajali: Ladan ya mutu a cikin Masallaci yayin jiran lokacin kiran Sallar Asuba

- Burin duk wani Musulmi shine ya cika da kalmar da shahada ko kuma ya mutu cikin hidimar addini

- Ladanin Masallacin Masjid Al Sulaiman dake Jeddah, Abdul Haq al Halabi, dan asalin kasar Syria dake zaune a kasar Saudiyya, ya yi kyakyawan karshe

- Dattijon, ya mutu yayin da yake zaune yana karatun Alqur'ani mai girma kafin lokacin kiran Sallar Asuba ya cika

Ladanin Masallacin 'Masjid Al Sulaiman dake' Jeddah a kasar Saudiyya ya mutu yayin jiran lokacin kiran Sallar Asuba. Ladanin mai suna Abdul Haq al Halabi ya mutu yayin da yake zaune yana karatun Alqur'ani mai girma kafin lokacin kiran Sallah ya cika.

Abdul Haq al Halabi dan asalin kasar Syria ne amma ya shafe fiye da shekaru 40 yana zaune a kasar Saudiyya.

Dattijon, mai shekaru 60 a duniya da 'ya'ya biyu maza; Khaldoun da Anas, da 'ya'ya uku mata, ya kasance mai hidima ga addini da kuma yawan son karatun Alqur'ani da nuna tsoron Allah.

Ya shafe shekaru 40 yana hidima a dakin Allah, wurin da ya mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel