Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa Alkalin tarayya, Justis Ibrahim Maikaita Bako rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa Alkalin tarayya, Justis Ibrahim Maikaita Bako rasuwa

Wani alkalin kotun tarayya, Justis Ibrahim Maikaita Bako, ya rasu a safiyar ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu a wani asibitin Abuja sakamakon raunuka da ya ji a wani hatsarin mota da ya ritsa dashi a makon da ya gabata.

A tuna cewa hatsarin mota ya cika da alkalin a hanyar Funtua-Kankara da ke jihar Katsina a ranar 4 ga watan Janairu.

Majiyarmu ta Daily Trust ta ruwaito cewa an dauki Justis Bako wanda ya ji mummunan rauni zuwa Abuja domin samun kulawar likitoci inda ya mutu a safiyar yau Lahadi a asibitin Cedar Crest, Abuja.

Da yake tabbatar da mutuwar, babban alkalin jihar Katsina, Justis Musa Danladi ya ce: “Marigayi Bako ya rasu da misalin karfe 6:00 na safe a Cedar Crest, Abuja biyo bayan wani hatsarin mota a ranar Juma’a, makon da ya gabata inda ya ji mukmunan raunuka a baya da wuya.”

Ya Kara da cewa “ya kasance a sashin kulawa ta ICU inda likitoci suka yi kokari daidaita shi kafin a fita dashi kasar waje don magani.

KU KARANTA KUMA: Giwa ta fadi: Wani tsohon gwamna na kwance da shanyewar barin jiki, yana neman kudin magani

“An kuma yanke shawarar yin jana’izarsa tare da binne shi a Abuja bayan sallar Azahar. Wannan rashi ne babba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel