Rikicin Boko Haram: Zulum ya bawa sojoji da 'yan sanda motoci guda 70 na aiki

Rikicin Boko Haram: Zulum ya bawa sojoji da 'yan sanda motoci guda 70 na aiki

- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Babagana Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 70

- Wannan kyautar ta biyo bayan kara kamari da rashin tsaro yake yi a jihar ta Borno

- Gwamnan ya bayyana cewa hakkin shi ne ya kare dukiyoyi da rayukan ‘yan jihar tare da tabbatar da zaman lafiya

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Juma’a ya bayar da motoci 70 ga rundunar sojin Najeriya tare da wasu hukumomin tsaro don taimakawa aiyukansu a jihar.

A taron da aka yi a Maiduguri, Zulum ya mika ababen hawan ga dukkan shuwagabannin tsaron da suka hada da rundunar sojin Najeriya, ‘yan sanda, jami’an tsaron hadin guiwa da kuma mafarauta.

Gwamnan ya yi wannan karamcin ne a lokacin da ake tsaka da matsalar tsaro a jihar.

Boko Haram da ISWAP a makonnin da suka gabata sun dinga kai hare-hare a kan manyan hanyoyi da kuma yankuna na jihar.

A cikin kwanakin nan ne aiyukan ta’addancinsu yafi kamari a kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri, wanda a da yafi tsaro a jihar. An kashe matafiya masu tarin yawa tare da kuma jaim’an tsaro a kan hanyar.

A ranar Talatar da ta gabata ne mayakan suka hari tawagar babban kwamandan Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi a kan babban titin Kano zuwa Maiduguri, amma basu samu nasara ba.

KU KARANTA: Iran ta bayyana cewa ita ta harbo jirgin Ukraine da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 176

A ranar Alhamis kuwa da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka kai wa matafiya hari har suka sace bakwai daga ciki a kan babbar hanyar Kano zuwa Maidugurin.

A makon da ya gabata ne kuwa gwamnan jihar ya fusata da lamurran sojojin dake kan hanyar. Ya zargesu da karbar cin hancin N1,000 daga mataifiyan da basu da katin shaidar dan kasa, lamarin da yace yana kawo babbar barazana ga tsaron jihar.

A yayin bikin karbar motocin 70 da gwamnan ya baiwa jami’an tsaron, wanda aka yi a fada sarkin Borno, Gwamnan yace “Ina yawan fada cewa wannan mulkin ba zai yi kasa a guiwa ba wajen daukar mataki don dawo da zaman lafiyar jihar nan. Ya zama wajibi gareni a matsayin shugaban tsaro na jihar nan da in kokarta wajen tsare rayuka da dukiyoyin jama’a” cewar Zulum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel