2023: Akwai yiwuwar mace ta maye gurbi na - El-Rufai

2023: Akwai yiwuwar mace ta maye gurbi na - El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce akwai yuwuwar mace ta gajesa yayin da kuma ya musanta zabar wanda zai maye gurbinsa a jihar a 2023. Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin da wasu mutane ke ta tunanin cewa namiji ne zai maye gurbinsa tare da wata mace a matsayin mataimakiya kamar yadda yayi da Hadiza Balarabe.

Amma kuma yace kamar dai yadda ya sani, yayi wuri da ya fara maganar zaben 2023, cewa da Ubangiji ne kadai ya san wanda zai maye gurbinsa a matsayin gwamnan jihar.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar, kuma jihar ke lura da lamurransa, ya ce mutane 10 ne a halin yanzu suka bayyana bukatarsu ta maye gurbinsa.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umurnin gina gidaje 1,000 a jihar Borno

Martanin gwamnan ya biyo baya ne bayan yaduwar jita-jita a kafafen sada zumuntar zamani a kan yadda ya zabi daya daga cikin hadimansa don ya gajesa.

"Naji abubuwa da yawa da mutane ke cewa a kan na zaba wanda zai gajeni. Bani da kowa a zuciyata da nake tunanin zai maye gurbina. Ina da mutane da yawa dake karkashina dake fatan maye gurbina saboda duk sun cancanta, amma babu wanda yake rai na. Zan iya cewa babu," in ji gwamnan.

Ya kara da cewa, "A bar talakawa su zaba shugabansu da kansu kuma ku tuna, Ubangiji ne kadai zai iya zaben shugaba na gaba. Na fita ne tare da neman yardar mutane kafin su zabe ni. Toh don haka kowa ya fita don neman goyon bayansu. Addu'a ta a kullum ita ce Allah ya zaba mafi alkhairi wanda zai kai jihar gaba." in ji El-Rufai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel